Yakamata Ayi Adalci Duk Wanda Yayi Laifi Doka Ta Hukunta Shi

Aiyukan kotun da’ar ma’aikata, a cewar jami’an kotun na gudanar batare da daukar hankalin jama’a ba,

A taron yaki da cin hanci da asusun Korad Adnauer, ya gudanar a Abuja masu jawabai kan kawo misali da shariar,Bukola Saraki, inda da yawan su ke nuna rashin amincewa da yunkurin sauya dokar kotun da’ar ma’aikata dake sauraren shariar. wasun su na ganin cewa ba Saraki, kadai ke da irin wanna laifin ba.

Shugaban jami’yyar Labour Abdulrazak Salami, yace “duk wanna siyasa ce, domin idan aka ce da an kama Bola Tinubu, an yimas hukumci aka ce anyi kuskure toh, kotu irin wannan in dai suka tabbatae cwa sun yi kuskure, toh sai sun sake gyara kansu.”

Shima sakataren jam’iyyar NCP, Yunusa Tanko, yana da ra’ayi mai kama da wannan, inda yake cewa “ In aka lura bashi kadai bane a ciki yakamata wasu Gwamnoni a lokacin sa dukkan su ne yakamata a bincika , dama an ce watakila saboda ya riga ya sabawa ita jam’iyyar nasa ne ko kuma shugaban kasa shi yasa ake bincikar sa, ga Bola Tinubu, shima an samesa da irin wannan amma an sake shi.”

Uwar kungiyar kwadago tace tana goyon bayan zamar kotun ma’aikatar kan Saraki, inji jami’ain kungiyar Komrade Nuhu Toro, yana mai cewa” kamar idan aka je gidajen yarin Najeriya, za’a samu barawon Akuya, an tsare shi kafin ma aka shi kotu ta tabbatar ko yana da laifi ko ba shida laifi, amma sai ka samu manya manyan shuwagabanin mu wadanda aka tabbatr suna da laifi amma ayi tayin juye juye ba’a so a fadi gaskiyar alamarin domin a hukunta su saboda haka tuni muka yi watsi da kwaskwarimar da ake son yi da cewa yakamata ayi adalci duk wanda yayi laifi doka ta hukunta shi.”

Aiyukan kotun da’ar ma’aikata, a cewar jami’an kotun na gudanar batare da daukar hankalin jama’a ba, wannan sharia ta Sarki, dake da manyan lauyoyi karkshin Kanu Agabi, na tsayin Dakar bayanai na kariya.

Your browser doesn’t support HTML5

Yakamata Ayi Adalci Duk Wanda Yayi Laifi Doka Ta Hukunta Shi - 2'17"