Jami'an kasar suka ce sai tayiwu wannan adadi ya karu, domin har yanzu akwai mutane fiyeda dari biyu wadanda har yanzu ba'a san inda suke ba.
Masu aikin ceto daga kasashen yankin Pacific suna amfani da wani kayan aiki na zamani, da karnuka, da kuma hannayensu suna tono baraguzan gidaje da shaguna, suna kasa kunne su ji motsin ko akwai wani da rai dake neman a ceto.
An zakulo wasu mutane daransu daga karkashin baraguzan, sai dai hukumomin kasar suka ce kiraye kirayen neman taimako da woyoyin celula da wadanda gine ginen suka danne suna raguwa.
Tuni dama tattalin arzikin kasar yake fuskantar matsanancin komada sabili da faduwar farashin mai a kasuwannin duniya.
Jiya Talata shugaban Amurka Barack Obama, ya bugawa shugaba Correa domin ya mika ta'ziyyar Amurkawa saboda rashin rayukar da girgizar kasar ta haddasa. Ya baiwa shugaban na Ecuador tabbacin Amurka zata yi bakin kokarinta wajen taimakawa kasar ta sake farfadowa.