An Tasa Keyar Mutane 8 Zuwa Gidan Yari Saboda Cogen Jarabawa

Ma'aikatan kiwon lafiya

An yi karin haske akan sunayen mutanen da aka cafke saboda zarginsu da coge a jarabawar daukan ma’aikatan kiwon lafiya.

Hukumomin shara’a a jamhuriyar Nijer sun yi karin haske akan sunayen mutanen da aka cafke saboda zarginsu da coge a jarabawar daukan ma’aikatan kiwon lafiya.

A wani taron manema labarai da ya kira mai gabatar da kara na Gwamnati Maman Tasiu Isa, ne ya tabbatar da haka gabanin tusa keyar mutane 8 zuwa gidan yari kafin a gurfanar da su gaban kuliya.

Yana mai cewa sai da aka bincika takardun sakamako 28,000 aka sami kurakurai dayawa bayan haka mutane dayawa sun kai kara. An samu wasu da basuyi jarabawar ba amma sun samu, an kuma samu wasu da suka yi jarabawar amma basu samu sakamakon kirki ba amma a sauya an basu babbar sakamako saboda haka dole ne a dauki mataki a kasa.

Ya kara da cewa kurakurai da aka samu sun isa a soke jarabawar domin bai kamata ba ace an dauki mutanen da basu cancanta ba a kowane irin aika balema ace kiwon lafiyar mutane.

Your browser doesn’t support HTML5

An Tasa Keyar Mutane 8 Zuwa Gidan Yari Saboda Cogen Jarabawa - 2'22"