Hukumar kula da da’ar ma’aikata a karkashin jagorancin mai sharia Danladi Umar, tace tana da hurumin sauraran karar da Gwamnatin tarayya ta shigar inda take tuhumar shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki, da yin laifuka tun zamanin da yake Gwamna a jihar Kwara shekaru goma sha uku da suka gabata.
Ana tuhumar Sanata Saraki da laifuka goma sha uku da suka hada da kin bayyana kadarorinsa zargin da ya musanta.
Daya daga cikin Lauyoyin dake kare Saraki, Mahmud Magaji, yace basu da wani haufi amma akwai wasu kura kurai a jawabin da aka yi game da takardar da suka shigar saboda haka za’a duba a gani idan ta kama a daukaka kara har zuwa kotun koli za’a yi.
Shima Lauyan Gwamnati mai tuhumar Saraki, Rotimi Jacobs, yayi korafi akan masu kare Saraki, inda yake cewa “ mun fisu hujja mai karfi yaya zasu ce ayi amfani da kundin tsarin mulki, na shekarar 1979, bayan muna da sabo na 1999, wannan ne ba zamu yarda ba.
Za’a fara saurarar karar ranar biyar ga watan Afrilu, Bukola Saraki, ya bayana a kotun tare da Sanatoci masu yawa da Lauyoyi masu kare shi su tamanin.
Your browser doesn’t support HTML5