Amurka, da kasar Kamaru sun rattaba hannu akan wata yarjejeniyar tsaro imnda Amurka, zata taimakawa kasar Kamaru karfafa tsaron masamman ma a tashohin jiragen sama da kan iyakokin ta da Najeriya ta arewacin kasa da ta gabashi inda take makwabtaka da jamhuriyar Afirka ta tsakiya.
Ta wadannan bangarori ne ‘yan Boko Haram da ‘yan tawayen jamhuriyar Afirka, ta tsakiya ke kutsowar kasar suna aikata aika aika.
Sufeto janar na ‘yan Sandar kasar Kamaru, Martin Mbarga Nguele, ne ya furta haka a lokacin da ya karbi bakuncin jakadar kasar Amurka dake Kamaru, Emmanuel Steven Rosa.
Sufeton janar din yace Amurka,zata sa naurorinta a tashoshin jiragen sama da iyakokokin kasar domin karfafa tsaro dama taimakawa dakarun tsaron kasar da labarai na siri.
Jakadan Amurka, Steven Rosa, yace anyi wannan yarjejeniya ne domin jami’an tsaron kasashen biyu suyi aiki kafada da kafada ya kara da cewa Amurka, zata taimaka gaya wajen dakile ‘yan ta’adda a kasar Kamaru baki daya.
A watanin baya Amurka, ta taimakawa Kamaru, da jami’an tsaro dari ukku, da kayayyakin yaki da makudan kudade domin yakar ‘yan Boko Haram.
Your browser doesn’t support HTML5