Shugabanin sashen Afirka na gidan Rediyon muryar Amurka dake birnin Washington suna gudanar da wata ziyara ta mako daya a Najeriya domin ganawa da manyan jami’a a Gwamnatin Najeriya da kuma gudanar da horo ga wakilan muryar Amurka.
Horaswan ya kunshi na wakilai masu kula da kiwon lafiya na Najeriya domin inganta ma’amalar dake tsakanin muryar Amurka da Najeriya da kuma ma’amalar dake akwai tsakanin muryar Amurka da ‘yan jarida a Najeriya dake samun horop na masamman akan yadda zasu inganta aiyukansu nay au da kullum.
A wurin ganawar da akayi ta baya bayan nan tsakanin Ministan watsa labarai na Najeriya Lai Mohammed da kuma Negussie Mengesha shugaban sashen Afirka na murya Afirka da Ms. Joan Mower mai kula da sashen horas da ma’aikata da kiwon lafiya da kuma Alhaji Aliyu Mustapha babban editan sashen Hausa inda aka yi nazari da tattauna akan hanyoyin da za’a bi domin inganta ma’amala tsakanin muryar Amurka da Gwamnatin Najeriya da wani sashen na ‘yan jarida a Najeriya wadanda ke cin muriyar horo na masamman da ake bayarwa a lokaci zuwa lokaci.
A wuri wannan ganawar Ministan watsa Labarai Lai Mohammed yayi tur da Allah wadarai da wani labari da aka wallafa a wata jarida a Najeriya na batanci ga muryar Amurka.
Yace ana iya ganin sa a matsayin ra’ayi ne kawai saboda kowa ya san irin rawar da muryar Amurka ke takawa wurin wayar da kan al’umar Najeriya.
Ministan yace tunani ne na wasu amma babu shakka muryar Amurka har yanzu tana gaba a kafofin watsa labarai da ‘yan Najeriya.
Najeriya ke yabawa kuma suke amincewa da aiyukansu doan haka abin juyaye ne ace wai muryar Amurka wadda ta dade tana gwagwarmaya akan zaman lafiya a Najeriya tana daukan wasu matakai na goyon bayan kungiyar ‘yan Boko Haram wanda duniya baki daya masamman Amurka take baiwa Najeriya hadin kai wurin yaki dasu.
Your browser doesn’t support HTML5