Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka da Koriya ta Kudu sun fara atisayinsu na shekara-shekara


Sojojin dake atisayi
Sojojin dake atisayi

Kowace shekara dakarun Amurka da na Koriya ta Kudu su kan yi atisayi domin shirin ko ta kwana lamarin da Koriya ta Arewa tace bana kam sai ta mayar da martani

Korea ta Kudu da Amurka sun fara wani atisayen soji na shekara-shekara, yayin da ake cikin wani yanayi na zaman dardar, dalilin wasu gwajegwajen manyan makamai da Korea ta arewa ta yi a ‘yan kwanakin nan.

Wannan atisaye wanda ake kira “Key Resolve and Foal Eagle” a turance, zai kasance shi ne atisaye mafi girma, wanda fiye da dakarun Korea ta kudu dubu 300 da na Amurka dubu 17 ke halarta.

Sa’oi kadan kafin fara atisayen, Ministan tsaron Korea ta arewa, ya fitar da wata sanarwa, wacce ta yi kashedin cewa za su kaddamar da hare-hare domin maida martani kan wannan atisaye, wanda ya kwatanta a matsayin wani mataki na kai mamaya ga kasarsu.

Sanarwar har ila yau, ta ce Korea ta arewa za ta kai harin nukiliya akan sansanin Amurka da ke kudanci da kuma daukacin yankin Pacific.

Sai dai kakakin ma’aikatar tsaron Korea ta Kudu, ya yi kira ga makwabciyarsu ta arewa, da su daina nuna taurin-kai yanha mai jaddada cewa za su maida da martani cikin hanzari ga duk wani hari da Pyongyang za ta kai musu.

XS
SM
MD
LG