Macizai, Musamman Mesa da Gamsheka, Sun Addabi Al'ummar Bangkok A Kasar Thailand

Dan kwana kwana, Pinyo Pookpinyo, yana nuna wata mesar da ta nade a jikinsa.

Daya daga cikin masu kama macizan ya damko kan wata mesa rana lahadi, 28 Fabrairu 2016.

Khun Pinyo ya kamo wata gamsheka ran lahadi 28 Fabrairu 2016

Khun Pinyo na ciro gamshekan da ya kama daga cikin wani akwati, ran lahadi 28 Fabrairu 2016

Khun Pinyo tare da wata gamsheka mai gfuba da ya kamo

An kamo wasu macizai da yawa kunshe cikin buhuna an kawo ma Khun Pinyo domin ya maida su can ciki daji ya sake.

Khun Pinyo yana bayanin wani maciji mai farautar beraye wanda ba ya da guba ga wata matar da aka kama macijin cikin gidanta

Mai dauikar hoton bidiyo na VOA, Zinlat Aung, na daukar hoton 'yan kwana kwana suna kokarin sakin wata mesa da suka kamo daga cikin birnin bangkok a daji.

Dan aikin kwana kwana na Bangkok, Pinyo Pookpinyo, yana kallon wasu macizai biyu Gamsheka da aka kama cikin birnin Bangkok za a sake su a cikin daji