Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Sin Ta Yi Kintacen Habaka Tattalin Arzikinta Zuwa Karshen 2016


Wata Ma'aikatar Kera Motoci a Kasar Sin
Wata Ma'aikatar Kera Motoci a Kasar Sin

Kasar Sin ta yi kintacen habaka tattalin arzikinta a shekarar nan ta 2016 da muke ciki, duk da matsalar tattalin arzikin da duniya ke fuskata.

Gwamantin Sin ta bayyana manyan matakan da zata dauka, wanda ta yi amannar zasu ci gaba da bunkasa tattalin arzikinta a matsayin kasa ta 2 a duniya mafi karfin tattalin arziki.

Wanda suke son tattalin arzikin nasu ya haura da akalla kaso 6 da digo 5 a shekarar nan ta 2015 da muke ciki, duk kuwa da tafiyar hawainiyar tattalin arzikin da ake samu a duniya da zaftare ayyukan da ake gani a masana’antu.

Firimiyan birnin Sin Li Keqiang ne ya bayyana haka, inda ya kara da cewa, sun maida hankali sosai ga kayayyakin da ake sarrafawa a cikin gida. Shima wani memba a kwamitin tuntuba na siyasar China yayi karin haske.

Da cewa an yi wannan kiyasin ne don a rage tsammanin da ya wuce kima. A bara dai, Sin ta cimma nasarar tattalin arziki da kaso 6 da digo 9, wanda haka ya dan yi kasa da kaso 7 bisa yadda suka so cimma.

XS
SM
MD
LG