WASHINGTON, DC —
Hukumomin kasar Brazil, sun sa kafa akan wasu kadarorin shahararren da wasan kwallon kafa nan na Barcelona, wato Neymar.
Kadarorin sun hada da jirgin ruwa , jirgin sama da wasu da dama da kudadensu yake kimanin Dalar Amurka miliya 50.
Wata kotun tarayya a Sao Paulo, babban birnin kasar ta Brazil, tayi watsi da daukaka karar da dan wasan gaba na Barcelona yayi na neman kotun ta takawa Gwamnati birki dagane da batun kadarorin na sa.
Shi dai Neymar, hukumomin Brazil, na tuhumarsa ne da laifin rashin biyan haraji daga shekarar 2011 zuwa 2013, wanda ya kai Dalar Amurka miliyan 16.
Lagaro Martins, na ma’aikatar haraji kasar ta Brazil, yace idan har Neymar , ya biya kudaden harajin da ake binsa toh tabashihakika babu maganar gidan yari.