shugaban ‘yan adawar kasar Liberiya, ya yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa bisa mutuwar fitaccen mutumin nan mai yawan sukar gwamnatin Liberia, wato Harry Greaves, wanda aka tsinci gawarsa a gabar ruwan da ke bayan ginin ma’aikatar harkokin wajen a Monrovia.
Wani kwararre mai bincike kan mamata na Amurka da gwamnatin Liberian ta haya domin yin bincike kan gawar, ya ce Greaves ya rasu ne bayan da ya ruwa ci shi.
Simeon Freeman, shugaba a bangaren ‘yan adawar kasar ta Liberia, wanda kuma ya yi wannan kira, na daya daga cikin mutanen da ake nema ruwa a jallo, bayan da ya zargi gwamnatin shugaba Ellen Johnson Sirleaf da mallakar wasu jerin sunayen mutanen da ke sukar gwamnatinta, wandanda kuma ya yi zargin ana so a kawar da su.
Shi dai Freeman ya na kalubalantar ikrarin da ake na cewa ruwa ne ya ci Mr Greaves.
A wata hira da ya yi da Muryar Amurka ta wayar talho, Freeman ya ikrarin cewa abinda ke faruwa a kasar ta Liberia na nuni da irin matsalolin da kasar ke fuskanta a fannin siyasa.