Wasu abubuwa da ke kara haddasa rashin cigaban kasa da al'uma, daya da ga ciki shine zalinci, danniya, handama da babakere, da dai makamantansu. A duk lokacin da za’a nemi al’uma dasu gudanar da wani aiki da yarjejeniya biyansu, to yazama wajibi a cika wannan alkawalin domin ta haka ne kawai za’a iya samun zaman lafiya cikin jama’a.
Wasu bayin Allah, da suke kai kokensu ga Allah, da kuma karamar hukumar Kunbotso a jihar Kano, da neman ta dubi Allah, ta biya su hakokinsu na aikin raba gidan sauro da suka yi a daukacin karamar hukumar. Wadannan bayin Allahn, suna koke da cewar an daukesu dasu gudar da wannan aikin dacewar idan sun kamala za’a basu hakkinsu, amma har yanzu kimanin watanni hudu 4 kenan kamar an shuka dusa, ba a mo ba labara.
Sun yi nuni da cewar a lokacin da aka neme su da su yi wannan aikin, an karbi lambar asusun ajiyarsu na banki, da cewar za’a sa masu wadannan kudaden, amma babu labari, kuma a zahirin gaskiya ko kudin da suka yi amfani dashi na mota, cin abinci da wasu lalurori, sun fitone daga aljihunsu.
Haka kuma sun ce suna cikin wani hali da yakamata a tausaya musu, wanda idan ba haka ba zasu shiga wani mawuyacin hali.