Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Shekaru 21 ya Fitar da Taswirar Kwaryar Kano


Taswirar Kwaryar Kano
Taswirar Kwaryar Kano

A duk daukacin rayuwar dan’adam kowane mahaluki nada nashi basirar da Allah yayi masa, sai dai ace taya mutun yayi amfani da irin tashi basirar? Yawan karatu bashi ke nuni da irin hazaka ko kaifin basira na dan’adam ba, sai dai ace taya mutun yayi amfani da nashi basirar.

Umar Muhammad Sulaiman, matashi ne dan shekaru ashirin da daya 21, wanda ya samu dammar kamala karatunshi na sakandire, amma bai samu dammar cigaba ba, saboda rashin halin yin hakan, amma Allah yasa yana da basira kwarai da gaske, don kuwa yayi wata rawar gani wajen fitar da zanen taswirar kwaryar cikin birnin Kano, wannan zanen nashi zaibama bako ko dan gari dammar fahimtar ya cikin garin Kano yake da yadda aka tsara garin kamar yadda masana suka fitar dashi.

Wannan wani abun kuzo again ne, ganin cewar gashi da kananan shekaru amma Allah, yabashi basirar iya zanen gari, da fitar da yadda kowane tsari wuri da yadda yakamata ace kowane abu yake.

Babban abun la’akari da wannan shine, yakamata matasa masu irin wannan basirar su dinga fitowa da irin tasu basira a kowane lokaci saboda mahukunta su sandasu, su kuma basu duk irin taimakon da yakamata, domin tahaka ne kawai za’a iya samu cigaba da yadace da kasa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG