Halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki yasa talakkawa da shugabanni suna kokawa shugaban kungiyar gwamnoni a Najeriya kuma Gwamnan jihar Imo Chief Rochas Okorocha yayi Karin bayani.
‘’Muna cikin damuwa da firgice bisa yadda kudaden shigan jihohi ke samun tasgaro da koma baya da yau ya kawo nakasu da koma baya ga rayuwar jamaar mu dole ne a dauki matakan gaggawa domin yantar da jihohi muna kira ayi wa tsarin tattalin arziki gyaran fuska domin lillike wuraren dake yoyo a baitulmalin Najeriya kuma mun hakkake cewa rashin iya gudanar da tattalin arzikin kasar nnan ne yakai kasar nan ga halin oni ‘yasu a gaskiya ma dai gwamnatin APC ta samu baitulmalin kasar kusan fayau’’.
Kalaman shugaban gwamnonin APC Kenan Chief Rochas Okorocha halin tattalin arzikin da Najeriya ke ciki har takai ga jihohi 18 basa iya biyan albashi to wai shin meke dalili.
Yushau Aliyu masanin tattalin arziki ne a Najeriya.
‘’Rashin bin kaidoji, kaidojin da ya shafi raba arzikin kasa na daya Kenan na biuyu kuma kaidoji wurin yin kasafin kudi da kuma rarraba ayyuka a jihar yadda gwamna a jiha yana karban kudi daga hukumar rabon arzikin kasa ta yadda a bashi a jihar sa kuma tan aba karamar hukuma to amma gwamna sai ya hada na jiha dana kananan hukumomi ya kashe kuma a kasa biyan albashi to akwai matsala, kaibama wanda kudaden da suke samu daga gwamnatin tarayya wanda ba zai isa a biya albashi ba’’
Duban yadda ake ta yamadidi ga bisa yadda kudaden da gwamnati ke kashewa musammam akan yan majilisu Dr Almaji Gaidam wani tsohon dan majilisar tarayya ne.
‘’Mu tashi gaba daya mu ceci wannan kasar babu kudin shiga kamar yadda aka saba, yan majilisa ba sai wai sashen mulki sunce mun yanke albashin mu mun rage abu kaza sannan su nemi yan majilsa suma suyi haka baa’a majilisa yakamata suma su dauki suyi jagorancin taimakawa kasar nan su rarrage duk wasu abubuwa da mutanen kasar nan basa jin dadi akan su kuma su kansu sun san abubuwa ne wadanda basa kan hanya’’.
Ga dai Hassan Maina kaina da Karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5