Al’umar musulmi a Najeriya da wasu kasashen duniya da dama, sun fara duban watan Ramadana wanda ake sa ran za a gani yau Laraba.
Da zaran an hangi watan, wanda ake sa ran za a gani a garuruwa da dama, musulmi za su dauki haramar fara azumin na watan Ramadana.
A wata sanarwa da ta fitar a jiya, hukumar da ke gudanar da bincike a sararin samaniya ta NASRDA a Najeriya, ta ba da tabbacin cewa yau Laraba 17 ga watan Yuni ake san ran za a ga watan na Ramadan.
Kakakin hukumar Mr. Felix Ale ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar wacce aka rabawa manema labarai.
Hakan na nufin ranar Alhamis za ta zama ranar farko ta watan Ramadana kamar yadda hukumomi ma Saudi Arabia suka sanar.
A na sa ran kasashe da dama za su dauki azumin a gobe Alhamis da zaran an ga watan a yau Laraba.