Da Gaske Pep Guardiola Zai Koma Manchester City?

Pep Guardiola, kwach na 'yan Bayern Munich

A bayan da kungiyar Bayern Munich ta sake shan kashi a karo na 4 a jere, jita-jita ta sake karfi cewa kwach Pep Guardiola yana shirin nade kayansa ya koma kungiyar Manchester City a Ingila.

A yayin da Bayern ke shirin karawa da FC Barcelona a zagaye na biyu na wasan kusa da karshe na cin kofin zakarun kulob kulob na Turai gobe talata, kungiyar Augsburg ta bi zakarun na Jamus har gida ta doke su da ci 1-0 ran asabar.

Wannan shine karo na farko cikin shekaru 24 da ake doke kungiyar Bayern sau hudu a jere, kuma a karon farko cikin shekaru 15, kungiyar ta kasa jefa kwallo ko daya a wasanni 3 a jere.

A yayin da wannan ke gudana ne sai ga rahotannin cewa Manchester City, mai bugawa a Firimiya Lig ta Ingila, tana kokarin janyo Guardiola mai shekaru 44 da haihuwa zuwa filin wasanta na Etihad domin ya maye gurbin Manuel Pellegrini a zaman kwach.

Shekaranjiya asabar, gidan telebijin na beIN Sports ya sanar ta Twitter cewa Guardiola yayi alkawari da baka cewa zai koyar da ‘yan wasan City a kakar kwallo mai zuwa.

Tancredi Palmeri, wakilin beIN Sports, ya buga ta Twitter cewa “Manchester City ta tuntubi Guardiola watanni biyu da suka shige, yace ba ya so. An sake tuntubarsa makonni biyu da suka shige, bai karba ba, amma kuma bai watsar ba. Ana ci gaba da tattaunawa.”

Rahotanni na cewa Manchester City ta gabatarwa da Guardiola tayin Euro miliyan 22 (kimanin Dalar Amurka miliyan kusan 33) a shekara domin ya taimaka mata wajen kawar da Chelsea daga saman teburin Firimiya Lig.

Daga can Ingila kuma, rahotanni na cewa manyan shugabannin Manchester City sun yi watsi da jita-jitar cewa an kulla wata yarjejeniya da Guardiola kan ya zamo kwach na kungiyar.