Sakamakon harin da 'yan kungiyar Boko Haram su ka kai a yankin Diffa a farkon wannan wata, hukumomin kasar sun ce an kashe 'yan kungiyar mayakan sa kai 513, an kama fiye da 300.
Sannan a cikin wannan adadi, 132, su na gidan kaso, yayin da 216 kuma su ke hanun jami'an da su ke yaki da ta'addanci a Niamey, babban birnin kasar.
Jami'in hulda da jama'a ta fuskar tsaro a kasar, Mallam Adali Toro, wanda ya bayyana haka, ya ce an kashe jami'an tsaron kasar 24, wasu 38 kuma su ka jikkata a gumurzun da aka yi da 'yan binidgar a yankin Diffa.
Sakamakon dokar ta bacin da hukumomi su ka kafa biyo bayan harin na Diffa, yanzu rayuwa ta sake, domin dokar ta bacin ta na aiki ne daga karfe 9 na dare zuwa karfe 6 na safe.
Kuma ta hana cinikin abubuawa da yankin ya saba saye da sayarwa daga Najeriya, da suka hada da kifi,da wasu kayan miya, da kuma man fetur.
Wannan dokar ta tilastawa 'yan yankin sake fasalin rayuwarsu da su ka hada da hana mata sanya hijabi, sakamakon harin kunar bakin wake da wata mace ta kai.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5