An yankewa matar tsohon shugaban kasar Ivory Coast Simone Gbagbo, daurin shekaru ashirin a gidan yari, a saboda rawar data taka a tarzomar bayan zabe a shekara ta dubu biyu da goma da kuma shekara ta dubu biyu da goma sha daya
Jiya Talata wata kotu a birnin Abidjan ta samu Simone da laifin sawa matakan tsaro kafar angulu, da shirya kungiyoyin yan banga a tarzomar data kashe mutane dubu uku. Ita da mijinta tsohon shugaba Laurent Gbagbo, sun kalubalanci sakamakon zaben da Allasane Ouattara ya lashe a shekara ta dubu biyu da goma.
To amma kuma, kungiyar dake hankoron kare hakkin jama'a ta Human Rights Watch, tace ya kamata gwamnatin Ivory Coast ta dankawa kotun kasa da kasa Simone Gbagbo, inda ake cajin ta da laifin musgunawa bani Adamu
Haka kuma kungiyar tayi kira ga gwamnatin Ivory Coast data hukunta dukkan laifuffukan da aka zargi sojojin dake biyaya ga shugaba Ouattara sun aikata a lokacin rikicin.