Ana Iya Sanya Cristiano Ronaldo A Jerin Gawurtattun 'Yan Kwallon Kafar Duniya Kuwa?

Cristiano Ronaldo dai bai taba lashe kofin kwallon kafar duniya ma kasarsa Portugal ba

A bayan da Cristiano Ronaldo ya zamo gwarzon kwallon kafa na shekarar 2014 a jiya litinin, masana tamaula da dama sun fara tunanin irin matsayin da zasu saka shi ganin cewa shi da wasu ‘yan wasa kwaya hudu kawai suka taba lashe wannan kambi akalla sau uku.

Tambaya a nan ita ce: shin za a iya sanya Ronaldo cikin jerin ‘yan wasan kwallon kafa da suka fi bajimta a duniya?

Daga jiya litinin zuwa yau talata, masana tamaula da dama sun yi ta sharhin cewa muddin dai Cristiano Ronaldo, har ma da Lionel Messi, basu lashe kofin kwallon kafar duniya ma kasashensu ba, to kuwa ba zai yiwu a sanya su cikin jerin mahsahuran ‘yan wasa irinsu Diego Maradona ko Pele ba.

Idan har nan da watanni 12 Ronaldo ko Messi dayansu ya zamo zakaran kwallon kafa na duniya, to su biyun a hade zasu zamo ‘yan wasa biyun da suka fi lashe wannan kambi na Ballon d’Or.

Sai dai duk da haka, wannan ba zai yi tasirin kirki ba idan har a cikinsu din babu wanda ya taba lashe kofin duniya ma kasarsa. Ronaldo shi ne kyaftin na kasar Portugal yayin da Messi shi ne kyaftin na Argentina.