Tun daga lokacin da aka fara rade-radin cewa Chelsea tana kokarin cire zunzurutun kudi har Euro miliyan 250 da aka Makala jikin kwantarakin dan wasan FC Barcelona, kuma dan Argentina, Lionel Messi, domin ta saye shi, an samu rahoyton cewa akwai wani amininsa ma dake kokarin janye shi zuwa Stamford Bridge.
Cesc Fabregas dan kasar Spain, aminin Messi ne a lokacin da suke bugawa a Barcelona, kuma an ce yana iya janyo ra’ayinsa kan ya koma Chelsea shi ma kamar yadda Fabregas yayi.
Sai dai kuma, Fabregas yace a’a, babu gaskiya a wannan labarin na cewa yana kokarin janye Messi daga Barcelona, kuma labaran da ake yadawa cewa shi kansa Messi bay a jin dadi a Barcelona, ba gaskiya ba ne.
Haka shi ma kansa Messi ya karyata rahotannin cewa yana kwadayin komawa Chelsea ko Manchester City, wabi bisa dalilin cewa shi da wasu ‘yan wasa ba su jin dadin manajansu Luis Enrique.
Messi ya fadawa gidan telebijin na FC Barcelona cewa, babu inda za shi, kuma duk maganganun cewa ya tattauna da Chelsea ko City, karya ne.