Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cristiano Ronaldo Shi Ne Zakaran Tamaula Na Duniya A 2014


Kyaftin-kyaftin na kungiyoyin kwallon kafa na kasashen duniya da masu koyar da su da kuma 'yan jarida sun hadu sun zabi Cristiano Ronaldo na kungiyar Real Madrid, kuma dan kasar Portugal, a matsayin zakaran kwallon kafa na duniya a shekarar 2014.

Ronaldo ya doke mai tsaron gidan Bayern Munich, Manuel Neuer, da dan wasan gaba na FC Barcelona, Lionel Messi, wajen lashe wannan kambi mai tasiri da ake kira Ballon d'Or.

Ronaldo ya samu nasara sosai a wasanninsa a 2014, inda ya jagoranci Real Madrid wajen lashe kofin zakarun kulob-kulob na Turai ta hanyar jefa kwallaye har 17.

Bayan nan, ya jagoranci Real Madrid wajen lashe Copa del Rey ta kasar Spain, duk da cewa bai buga wasan karshe da suka yi da Barcelona ba saboda ya ji rauni.

Ronaldo, mai shekaru 29 da haihuwa, ya zamo wanda ya fi jefa kwallaye cikin raga a wasannin lig-lig na Spain, La Liga, inda ya jefa kwallaye 31 a wasanni 30 da ya buga. Shi da Luis Suarez sun kuma zamo zakarun Takalmin Zinare na Turai, watau wadanda suka fi jefa kwallaye a raga a duk Turai.

Wannan shi ne karo na uku da Ronaldo yake zamowa zakaran kwallon kafa na duniya.

Kuma ya zamo dan wasa na 7 a tarihi da ya taba lashe wannan kambi akalla sau biyu a jere a bayan 'yan wasa irinsu Johan Cruyff, Kevin Keegan, Karl-Heinz Rummenigge, Michel Platini, Marco van Basten da kuma Lionel Messi.

XS
SM
MD
LG