A halin yanzu dai bayanai na nuna cewa an sami asarar rayuka da dukiya yayin da aka tura karin jami’an tsaro.
Wani mazaunin garin Wukari wanda ya so a sakaye sunanshi cewa yayi “walLahi mu kanmu baza mu san meke faruwa ba, saboda harbe-harbe ne suka fara jiya, daga cikin anguwannin Jukun, daga bisani kuma sai kone kone”.
“Akwai mutane goma sha, wadanda suka mutu”, mutum ya kamala.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, ASP Joseph Kuji, yace ana binciken wannan lamari.
Kuji yace “a take, an tura ‘yan sanda da mobilawa da sojoji, yanzu da muke magana, kura ya lafa.”
Korafin da jama’a keyi na cewa jami’an tsaro basu isa ba wadannan yankuna ba, yasa ASP Joseph Kuji ya mayar da martani.
“Wannan magana ne kawai, jami’an tsaro sun taka rawar gani a wannan abunda ya faru.”
Jama’ar Jihar Taraba sun kwana biyu suna ganin tashe-tashen hankula masu nasaba da kyamar al-ada ko addini ko kabila.
Your browser doesn’t support HTML5