Wasu ‘yan majalisar dattijan Najeriya sun rattaba hannu kan takardar bayyana aniyarsu ta tsige shugaba Goodluck Jonathan daga kan kujerarsa ta shugaban kasa. Sanata Alkali Abdulkadir Jajere daga Jihar Yobe, yace yana daya daga cikin wadanda suka sanya hannu kan wannan takardar aniya, ya kuma bayyana dalilansa. Akwai ‘yan majalisar wakilan Najeriya ma da dama da suka bayyana aniyarsu ta tsige shugaba Goodluck Jonathan daga kan mukaminsa.
A Jamhuriyar Nijar, gwamnatin firayim minista Briji Rafini ta tsallake rijiya da baya a lokacin da ‘yan adawa a majalisar dokokin kasa suka nemi a kada kuri’ar tsige ta. Dan majalisa Lamido Moumouni na jam’iyyar adawa ta MNSD yace duk da cewa ba su samu nasara ba, duniya ta san halin da ake ciki. Shi kuma dan majalisa Tijjani Abdulkadir na wata gamayyar ‘yan adawa da ake kira IRN cewa yayi ai ba a yi kuri’ar ba ma, magudi kawai aka tabka. A bayan da gwamnatinsa ta tsallake rijiya da baya, firayim minista Rafini ya ja numfashi yace da ma ‘yan hana ruwa gudu ne ke neman yin kafar ungulu, amma kuma ba zasu iya tare wannan ruwan ba…
Gwamna Kashim Shettima na Jihar Borno, yace in Allah Ya yarda an kusa kawo karshen abinda ya kira wannan hauka dake wakana a jihar da makwabciyarta. Gwamnan ya fadi hakan ne a bayan da yaje ya duba wadanda suka ji rauni a sanadin tagwayen hare-haren bam a Maiduguri.
Your browser doesn’t support HTML5