Kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta bi sahun masu yin kira ga jama’a da su fara tashi su na kare kawunansu daga hare-haren ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a Najeriya.
Dr. Khalid Abubakar Aliyu, sakataren kungiyar na kasa, yace "mun gaji da gafara sa, har yanzu ba mu ga kaho ba, kuma m=mun gaji da zub da jinin al'ummarmu, da matasanmu tare da kashe harkokin kasuwancinmu."
Yace dokokin najeriya ma sun ba kowa ikon kare kansa idan har hukumar da aka dora ma nauyin hakan ta kasa, domin babu ta yadda mutum zai tsaya kawai har a zo a kashe shi.
Yace ba wai yana kiran mutane da su dauki doka a hannunsu ba ne, amma kare kai ya zamo wajibi.
Sannan yayi rokon da a ci gaba da yin addu'o'i, musamman al-Qunut, a masallatai a duk lokutan salloli farillai domin Allah Ya kawar da wannan masifa tare da murkushe masu haddasa ta.
A wani labarin dabam kuma, an yi hasarar dukiya mai yawa, amma kuma babu hasarar rayuka a lokacin da wuta ta kama wasu shaguna a bakin kasuwar Kumo dake Jihar Gombe.