Allah Ya Isa Mana Kan Duk Wani Mai Hakkin Tsaro A Najeriya In Ji Wamakko

Gwamna Alu Magatakarda Wamako

Gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko na Jihar Sokoto yayi tur da matakan da 'yan sandan Najeriya suka dauka na kokarin hana shugaban majalisar wakilan tarayya, Aminu tambuwal, da 'yan majalisar shiga ciki a jiya alhamis.

Gwamna Wamakko, yace wannan babban abin kunya ne na gwamnatin Goodluck Jonathan, abinda ya zubar da mutuncin Najeriya a idon duniya da kuma idon 'yan Najeriya su kansu.

Gwamnan na Sokoto, yace babban abin kunya ne ga Najeriya a ce 'yan tauri ne zasu yi ma sojoji jagora wajen yakar 'yan ta'adda.

Gwamna Wamakko yace Allah Ya isar ma dukkan 'yan Najeriya a kan duk wani mai hakkin tsaro a kasar.

Your browser doesn’t support HTML5

Allah Ya Isa Mana Kan Duk Mai Hakkin Tsaro In Ji Gwamna Wamakko - 2'29"