Ra'ayoyin Masu Sauraro Kan Halin Da Ake Ciki A Arewa

Hadi Tsohon sarki daga garin Daura a Jihar Katsina da kuma Muhammad Dan Malam Direba Oshodi sun bayyana ra'ayoyinsu kan matsalar tsaron arewa
A ci gaba da bayar da dama ga masu sauraronmu da su bayyana ra'ayoyinsu a kan abubuwan da suke gudana a yankin arewacin Najeriya, wadannan masu sauraro biyu su na daga cikin wadanda suka kira layukanmu, suka bar ra'ayoyinsu kan kafa dokar-ta-baci da kuma umurnin sakin 'yan Boko Haram, musamman mata, da ake tsare da su.

Hadi Tsohon Sarki na Kofar Arewa a garin dauran Jihar Katsina ya bayyana ra'ayin cewa kamata yayi dukkan talakawan arewa, ba wai na Borno da Adamawa da Yobe kawai ba, su dage da addu'a domin ganin karshen wannan masifa, domin a ra'ayin nasa, dokar-ta-baci da kuma kafa kwamitin ahuwa ko sasantawa ba su ne zasu iya kawo karshen wannan lamarin ba.

Shi kuma Muhammadu Dan Malam Direba Oshodi, ya gode da matakin sakin 'yan Boko Haram dake tsare, ya kuma roki 'ya'yan kungiyar da su ajiye makamansu domin a samu zaman lafiya a kasa, yana mai cewa wannan masifar yanzu tana shafar kowa da kowa ne a kasa.

Your browser doesn’t support HTML5

Hadi Tsohon Sarki, Kofar Arewa, Daura Yana Kiran Talakawa Su Dukufa Ga Addu'a - 00:52


Your browser doesn’t support HTML5

Muhammadu Dan Malam Direba Oshodi Yana Fadin Ra'ayinsa Kan Sakin 'Yan Boko Haram - 00:54


Duk mai sauraron dake son jin ra'ayinsa a wannan dandali, yana iya kiran lambarmu ta barin sako, watau +1 202-205-9942, idan ya ji an dauka sai ya danna 12 sai kiran ya shiga wurin ajiyar sakon Sashen Hausa, sai a dakata za a ji gaisuwa da Hausa, idan an kammala gajeruwar gaisuwar, za a ji wata kara, to sai a fara magana, duk abinda aka fada na'ura zata nade.

A yi magana da karfi, ba tare da tsattsayawa ba. Mun gode.