Wakilinmu a birnin Tarayyar Nijeriya Abuja, Nasiru Elhekaya, ya aiko ma na da rahoton cewa a Nijeriya, wadda akasarin jama'arta sun fi dogara ne kan wutar lantarki, abin da gwamnati ta fi alkawarin gyarawa ita ce wutar lantarki. Nasiru ya ruwaito karamin Ministan Kudi Yarima Ingawa na bayyana cewa kwanan nan kararrakin janaretocin wuta za su zama tahiri a Nijeriya. Ya ce tuni aka girke wani dirkeken injin din wutar lantarki a Kokin Gurara, wanda zai samar wa Kaduna wuta sannan daga nan kuma ya yada wutar zuwa sauran jihohin kusa.
Shi ko Alhaji Muhammadu Magaji, Sakataren Yada Labaran Kungiyar Manoman Nijeriya, ya ce tsarin da ake bi wajen rabon taki ya fi na gabanin lokacin dimokaradiyya; yayin da shi kuma wani mazaunin arewa maso gabashin Nijeriya mai suna Sabo Imamu Gashuwa ke cewa ana ta daukar kudaden da ya kamata a yi amfani da su wajen ayyukan cigaba ana ta bararwa da sunan matakan tsaro. Su kuma nakasassun Nijeriya sun yi barazana ce cewa nan gaba ba su ba wanda ya ki tafiya da su. Alal misali, wani nakasasshe mai suna Aminu Tudun Wada ya ce nan gaba za su mara baya ne ga duk wanda ya ba su Mataimakin Shugaban Kasa ko kuma Mataimakin Gwamna.