Shugaban ya ce a bayan samar da wutar lantarki da karfinta zai iya kaiwa Megawatt 700, madatsar ruwan da za a gina zata kuma samar da ruwa ga gonaki masu yawan gaske domin gudanar da ayyukan noman rani a wannan yanki.
An yi kiyasin cewa za a kashe kudi sama da naira miliyan dubu 162 wajen gina wannan tashar wutar lantarki.
Gwamna Babangida Aliyu na Jihar Neja, da manyan sarakuna da jami'an gwamnati suka tarbi shugaba Jonathan a wurin bukin da aka gudanar na kaddamar da wannan aikin, daga inda wakilin sashen Hausa, Mustapha Nasiru Batsari ya aiko da wannan rahoto.