Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zuma Ya Ce Rashin Adalci Ne a Ce Ya Yi Murabus


Shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma a lokacin da ake hira da shi a talbijin
Shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma a lokacin da ake hira da shi a talbijin

Yayin da majalisar dokokin Afirka ta Kudu ke shirin kada kuri'a kan makomar shugabancin Jacob Zuma, shugaban ya kare kansa a wata hira da aka yi da shi.

Shugaban Arrika ta kudu Jacob Zuma, wanda yake tsaka mai wuya ya kare kansa, a wata hira da aka yi da shi kai tsaye ta tashar talabijin a yau Laraba.

Zuma ya ce “babu adalci” a matsin lamba da ake yi masa na ya yi murabus, kuma ba’a fada masa wanne laifi ya yi ba.

Da yake magana ta tashar talabijin ta kasar da ake kira SABC a takaice, Zuma ya ce ya gana da manyan shugabannin jam’iyyar ANC mai mulkin kasar a karshen makon jiya, kuma ya amince da cewa zai yi murabus amma wanda za’a jinkirta.

Ya ce ya ba da shawarar ya ci gaba da aiki har zuwa watan shida.

Amma shugabannin na ANC sun ki su amince da wannan tayin d a ya yi masu, suka kuma bukace shi da ya yi murabus nan take.

Jam’iyyar ta ce majalisa za ta kada kuri’a yanke kauna kan shugabancinsa gobe Alhamis idan bai sauka kafin lokacin ba.

“Ba za mu ci gaba da sa Afirka ta kudu ta jira ba,” inji ma’ajin jam’iyyar, Paul Mashatile.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG