Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyya Mai Mulki A Afirka Ta Kudu Ta Yiwa Shugaba Zuma Kiranye


'Yan Jam'iyyar ANC da ke neman Shugaba Zuma ya sauka.
'Yan Jam'iyyar ANC da ke neman Shugaba Zuma ya sauka.

Jam'iyya mai mulki (ANC) a Afirka ta kudu ta ce ta tattauna da Shugaban kasar Jacob Zuma akan shawarar da ta yanke ta yi masa kiranye amma ba ta ba shi wani wa'adin mayar da martani ba.

Jam’iyya mai mulki ta Afirka ta kudu ta yanke hukuncin yi wa shugaban kasar, Jacob Zuma kiranye daga matsayinsa na shugaban kasar, koda yake akwai alamun cewa shugaban ba shi da niyyar bada hadin kai ga wannan shirin.

A yau Talata ne sakataren Jam’iyyar ta African National Congress (ko A-N-C) Ace Magashule, ya bayyana haka a taron manema labarai cewa shuwagabannin jam’iyyar sun gana da shugaba Zuma, kuma sun fada masa hukuncin da suka yanke wanda ya ce, yana daga cikin dokokin tsarin mulkin jam’iyyar.

Kawo yanzu dai babu wani martani daga Zuma, amma Magashule ya ce yana sa ran shugaban ya mayar da martani zuwa gobe Laraba, ko da shike ya jaddada cewa jam’iyyar ba ta yankewa shugaban wani wa’adi ba.

Dokar tsarin mulkin kasar bata wajabtawa Shugaba Zuma amincewa da hukuncin jam’iyyar ba. Idan ya ki amincewa ya sauka, za a gabatar da batun a gaban majalisar dokoki ta kasar wadda zata iya tsige shi bisa kuri’ar rashin amincewa. Idan haka ya faru, shugaban jam’iyyar ANC Cyril Ramaposa ka iya kasancewa shugaban kasar Afirka ta kudu.

An dade ana zargin shugaba Zuma da laifukan cin hanci da rashawa wanda ke da nasaba da faduwar tattalin arzkin kasar Afirka ta kudu tun daga lokacin da ya fara mulkin kasar a shekarar 2009.

Cikin zarge-zargen da ake masa, masu suka sun ce shugaba Zuma ya yi amfani da kudin gwamnati dalar Amurka, miliyan $20, wajan gyara gidansa, da kuma ba wasu attajiran Indiyawa hurumin zabar ministocin kasar.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG