Haka kuma, sarkin ya bukaci hakimai da sauran masu sarauta da su tabbatar da cewa sai wadanda suke da sani da kuma izni za abari su yi wa'azi.
Sarkin yana magana ne a gaban dubban jama'a da suka halarci taron kolin zaman lafiya na shekara wanda masarautar ta saba gudanarwa kan addini da kuma ilmi.
Shi ma shugaban kwamitin da masarautar ta kafa domin wayar da kan jama'a game da harkokin addini a kasar Kwantagora, Kanar Sani Bello mai ritaya, ya jaddada muhimmancin ilmi na addini da na zamani a wurin taron, yana mai fadin cewa za a barsu a baya idan ba su dage wajen neman ilmin ba.
Kwamishinan harkokin addini na Jihar Neja, Alhaji Shehu Haruna, yace gwamnatin Jihar ta yi murna da irin wannan taro kuma tana bayar da cikakken goyon bayanta. Yayi kira ga sauran masarautu na jihar da su yi koyi da irin wannan mataki da masarautar Kwantagora ta dauka.
Wakilin Sashen Hausa, Mustapha Nasiru Batsari, ya aiko da cikakken bayani.