Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga-zangar Ma’aikatan Hukumar Tashoshin Ruwan Najeriya


LAGOS: Tashar jiragen ruwa dake Legas
LAGOS: Tashar jiragen ruwa dake Legas

Daruruwan ma’aikatan hukumar tashoshin jiragen ruwan Najeriya ne da hukumar ta yi watsi da su, suka gudanar da zanga-zangar lumana a gaban ofishin hukumar da ke Lagos, domin kira ga hukumar da kuma gwamnatin Najeriya na maida su bakin aiki da kuma biyansu hakkokinsu.

Ma’aikatan sun gudanar da zanga-zangar lumana ne domin nuna rashin jin dadinsu da halin ko in kula da hukumar tashoshin ruwan Najeriya ke nuna musu, kusan shekaru goma bayan sun kammala ‘daukar darasi a hukumar tashohin jiragen ruwan.

An gudanar da zanga-zangar ne domin jan hankalin hukumomin tashoshin jiragen ruwan, musamman ma shugabar hukumar Mallama Hadiza Bala Usman, na ganin ta ‘dauke su aiki maimakon sabbin ma’aikata da yanzu rahotanni ke cewa hukumar na ganawa da su domin ‘daukarsu aiki, duk kuwa da umarnin wata babbar kotun tarayya da ke Legas da kuma majalisar tarayyar ta bayar na cewa a dakatar da ‘daukar sabbin ma’aikatan, har sai an saurari kukan ma’aikatan da tun farko aka ‘dauka ta re da horas da su.

A cewar ‘daya daga cikin masu zanga-zangar yace sun fito ne domin neman hakkinsu a hannun ma’aikatar NPA, biyo bayan kwashe shekaru goma da aka yi duk da cewa sun mika kukansu duk inda ya kamata, amma shiru babu labari.

Manajan hulda da jama’a ta hukumar ta yi jawabi ga masu zanga-zangar, inda ta ce tayi imanin cewa kasancewar shugabar hukumar da ta ke ‘yar rajin kare hakkin bil Adama ce, za ta duba wannan kuka da masu zanga-zangar suka gudanar.

Domin karin bayani saurari rahotan Babangida Jibrin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG