Sai dai duk da cewa shugaban bai halarci taron ba, ya baiwa mataimakinsa, Farfasa Yemi Osinbajo, umurnin ya tattaro duk ayyukan dake bukatar amincewarsa zuwa gidansa domin ya yi aiki a kansu.
Ministan watsa labarai na Najeriya Alhaji Lai Muhammad ya bayyanawa manema labarai sakon bayan da majalisar ta kammala taronta na mako-makon.
To sai dai rashin kasancewar shugaban a wurin taron ya karfafa rade-radin da wasu 'yan kasar ke yi na cewa shugaban bas hi da lafiya kuma baya iya gudanar da ayyukansa na kasa kamar yadda ya kamata.
Kakakin fadar shugaban kasa ta Aso Rock, Malam Garba Shehu, yayin wata ganawa da Sashen Hausa na Muryar Amurka ya ce aikin shugaban kasa aiki ne na sa'o'i 24 a kowace rana, ya na mai cewa babu lokacin da za'a ce an daina aikin.
Malam Garba Shehu ya ce shugaban na da ofis a gida da bangaren fadar inda suke taro saboda haka yana iya aiki daga duk inda ya ga dama.
A cewar Shehu, shugaban ya ce zai huta ne yau amma ya umurci mataimakinsa ya tara duk takaradun da suke bukatar ya yi aiki a kansu ya kawo masa su gida.
Taron da ake yi a kowace ranar Laraba al'ada ce da aka kirkiro shi a yanayin tafiyar da harkokin mulkin Najeriya, ba wai doka ce ba
Amma duk ranar da shugaba yake son a yi taron ministoci za'a iya yi.
Dangane da lafiyar shugaban, Malam Garba Shehu ya ce babu wani uzuri da ya taso saboda lafiyarsa.
Amma lokacin da ya dawo daga jinya ya fada cewa zai dinga aiki a hankali har Allah ya sa bashi lafiya.
Ga rahoton Umar Faruk Musa domin jin karin bayani.
Facebook Forum