Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Tsoffin Manyan Ma'aikata da Gwamnatin Adamawa Sun Shiga Takunsaka


Mustapha Galadima shugaban Kungiyar tsoffin sakatarorin jihar Adamawa
Mustapha Galadima shugaban Kungiyar tsoffin sakatarorin jihar Adamawa

Tsoffin sakatarorin ma'aikatun gwamnatin Adamawa da gwamnati mai ci a yanzu, sun shiga takun-saka bisa ga rashin biyansu kudaden fansho duk da taimakon da jihar ta samu daga gwamnatin tarayya.

Kungiyar tsoffin manyan sakatarori wato permanent secretaries da ta kunshi akawun majalisar dokokin jihar da tsofffin cif joji da mai binciken kudi dama wadanda ke karbar dunkullealen –albashi, na kokawa ne da cewa gwamnatin jihar na nuna halin ko-in-kula game da halin da suke ciki a yanzu na rashin biyansu hakkokinsu na barin aiki.

Kamar yadda alkalumman kungiyar tsoffin ma’aikata a jihar ke nunawa a jihar Adamawa tsoffin ma’aikata na bin gwamnatin jihar albashin kudaden sallama sama da Naira biliyan 19.

Shugaban kungiyar tsoffin manyan sakatarorin wato permanent secretaries, Mustapha Galadima ya shedawa taron manema labarai a Yola fadar jihar cewa kungiyar ba ta anfana ko da kwandala ba daga tallafin da gwamnati tarayya ke rabawa jihohi na kudin "bail out" ko kuma Paris Club kamar yadda ake mai lakabi.

Shima wani tsohon sakataren dindin din, Alh. Abubakar Hassan ya ce bai kamata gwamnatin dake tutiyar kawo canji,ta mance dasu ba.

Kamar Abubakar Hassn shima Mr Emmanuel Vinjir da ya shafe shekara da shekaru yana bautawa gwamnatin jihar yace suma suna da hakki.

To sai dai kuma,gwamnatin jihar ta bakin kwamishinan yada labaranta Ahmad Sajo ta ce ba haka zancen yake ba.

A cewar kwamishinan, yanzu haka suna aikin tantance tsoffin ma'aikatan domin ganin wadanda suka cancanta su ci gajiyar kudaden sun samu hakkokinsu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG