Hukumar tace ayyukanta basu raunata ba ko a birnin Jos da ma wasu sauran biranen kasar inda ta karfafa matakan tsaro.
Shugaban hukumar Malam Habeeb Abdullahi shi ya shaidawa manema labarai a ofishinsa dake Legas. Yace sai dai shiga tashar ya dan kara tsanani ganin irin abun da ya faru a dipo na Folawuyo dake daf da tashar tasu. Ba hukumar ba ce kadai ta tsaurara matakan tsaro ba har ma da jami'an tsaro masu ruwa da tsaki a harkokin tsahar jirgin ruwan Najeriya musamman harkokin fitowa ko shigowa da kaya.
Dangane da ko abun da ya faru a dipo din Folawuyo ko zai iya karya gwiwar masu shigo da kaya daga kasashen waje shugaban hukumar yace su kan hadu da jami'an tshoshin kasashen Afirka ta yamma da ta tsakiya su yi muhawara tsakaninsu. Suna sanin duk inda jirgi ya fito da irin kayan da yake dauke dasu da inda zashi.
Shugaban hukumar yace sun samu nasara wurin shawo kan shigowa da muggan makamai. Duk wanda yake tunanen yin hakan dole yanzu yayi tunane sabili da matakan da suka dauka.
Ga rahoton Ladan ibrahim Ayawa.