Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga-Zangar Gamagari: Mutanen Da Ake Tuhuma Sun Suma A Gaban Kotu

Zanga-zangar Tsadar Rayuwa A Najeriya
Zanga-zangar Tsadar Rayuwa A Najeriya

Ana tuhumar mutanen, su 75 da shekarunsu na haihuwa ke tsakanin 12 da 15 da laifuffukan da suka shafi ta’addanci guda 10, da suka hada da yunkurin kifar da gwamnati da kuma zargin yin tawaye sakamakon rawar da suka taka a zanga-zangar gamagari.

Wasu daga cikin mutanen da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gurfanar a gaban Mai Shari’a Obiora Egwuata na babbar kotun tarayya dake Abuja sun suma.

Ana tuhumar mutanen, su 75 da shekarunsu na haihuwa ke tsakanin 12 da 15 da laifuffukan da suka shafi ta’addanci guda 10, da suka hada da yunkurin kifar da gwamnati da kuma zargin yin tawaye sakamakon rawar da suka taka a zanga-zangar gamagari.

Ana zargin cewar an kama mutanen ne a ranar 3 ga watan Agustan daya gabata kuma sannan suna tsare.

Kotun ta zauna ne domin fara sauraron karar tare da baiwa wadanda ake tuhuma damar amsa laifi ko akasin hakan sa’ilin da wasu daga cikinsu suka some, abinda sabbabawa Mai Shari’a Egwuata dage zaman kotun babu shiri.

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG