Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayyana cewar samar da tsarin demokradiya da zai tafi da kowa tare da ciyar da kasa gaba shi ne babban burin daya sa a gaba.
Ya bayyana hakan ne sa'ilin da ya karbi bakuncin Kwamitin Gudanarwar jam'iyyar APC na kasa a Alhamis din data gabata a Legas, inda ya bayyana goyon bayansa ga yunkurin kafa cibiyar nazarin harkokin ci gaban siyasa da jam'iyyar APC ke shirin yi.
"A baya tsarin demokradiya ya fuskanci dimbin kalubale , amma ina da yakinin cewar muna da kyakkyawar makomar kuma zamu tabbatar da hakan"
Ya kara da cewar, na kudiri aniyar talafawa kafuwar tsarin kwakkwarar tsarin demokradiya da ya ginu akan akidar ci gaba da tafiya da kowa sannan ta maida hankali akan kawar da fatara tare da sama 'ya'yanmu ingantaccen ilmi.
Shugaba Tinubu ya ci gaba da cewar, hadin gwiwa da sauran matakan gwamnati abu ne mai mahimmancin gaske kuma dole "in jinjinawa jagorancin jam'iyyarmu saboda dabbaka wadannan muradai masu mahimmanci".
Har ila yau, Shugaban ya ci gaba da cewar ana sa ran cibiyar ta rika gudanar da bincike mai zurfi tare da ilmantar da mambobin jam'iyyar APC game da ginshikan tsarin demokradiya da kyakkyawan jagoranci tare da fayyace siffofin jam'iyyar.
Sa'ilin da yake bayyana dmuwarsa game da karuwar yaran da basa zuwa makaranta a Najeriya, Shugaban ya shelanta cewar, "wajibi ne mu magance wannan matsalar ta hanyar samarda karin makarantu da daukar malamai aiki tare da samar da abinci akalla sau daya a rana ga daliban a bisa dacewa da akidar ci gaban da muka sa a gaba".
Dandalin Mu Tattauna