Karamin Ministan Tsaron Najeriya kuma tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bayyana hakan ne a wata kebbabiyar hira da Muryar Amurka a Abuja.
‘’Akwai kayyayaki na yaki sosai kuma muna ba da tabbaci ce wa, in Allah ya yadda za’a ga sakamako mai kyau. Kuma za’a rika tunkararsu duk inda su ke, duk dajin da suke a kai musu farmaki ba tare da ce wa sai an jira sun taho sun yaki al’uma ba’’, in ji Matawalle.
Karamin Ministan ya ce akwai alaka tsakanin jami’in tsaro sai dai matsalar da su ke fama da ita a wannan yaki da ta’adanci ita ce ta ‘’masu bada asirin jami’an tsaro wanda su ne babban matsalar’’ a cewar sa.
Matawalle dai ya jadada cewa, an dauki kwararan matakan kiyaye sake afkuwar irin iftila'in da ya faru a Kauyen Tudun Biri dake Jihar Kaduna a Najeriya.
Inda ya ce Shugaban Kasa, Bola Tinubu ya umurce su su ‘’tabbatar da adalci da kuma tabbatuwa ce wa matakin da za’a dauka, wayanda za’a ga karshen irin wayannan matsaloli ne’’, kuma ‘‘gwamnati ta dauki mataki kwakwara akan wannan abu’’.
Ya ce ta’aziyar da jami’in gwamanati suka kai ma wayanda iftila’in ya shafa da sadaukar da albashinsu ‘‘domin tabbatar wa duniya ce wa wannan abu da ya faru, ba wanda ya ji dadinshi’’.
Karamin Ministan ya kuma sha alwashin ce wa ‘’wannan abu ba zai sake faruwa ba’’ saboda an ‘’dauki mataki kwakkwara akan wannan, kuma za’a sanar da ‘yan Najeriya akan abunda ake ciki’'.
Latsa wannan bidiyo don jin cikkakiyar hirarsa da Halima Abdulra’uf.
Dandalin Mu Tattauna