Rundunar sojojin kasa ta Najeriya, ta ce mayakanta sun kashe 'yan ta'addar Boko Haram su 10, suka kama makamai masu yawa a wani fadan da aka gwabza a garin kangarwa dake yankin karamar hukumar Kukawa ta Jihar Borno.
Sanarwar da rundunar sojojin ta bayar, ta ce sojoji guda 3 sun rasa rayukansu a fadan da aka gwabza da maraicen alhamis har zuwa tsakar daren alhamis.
Darektan yada labarai na rundunar sojojin kasa ta Najeriya, Birgediya-Janar Sani Kukasheka Usman, yace 'yan ta'addar na Boko Haram da suka fito daga bakin gabar tabkin Chadi, sun far ma sansanin sojoji dake Kangarwa, inda suka yi ta arangama da sojojin bataliya ta 119 da kuma bataliya ta 133 ta zaratan sojoji har zuwa cikin daren alhamisar.
Yace sojojin sun samu nasarar fatattakar 'yan ta'addar tare da kashe 10 daga cikinsu, da kuma raunata wasu da dama.
Sun kuma kwato bindigogi, da gurneti, da mashin gan, da rediyon oba-oba, da Qur'ani da kuma tutar 'yan Boko Haram.
Sai dai kuma, Birgediya Janar Usman yace sojoji 3 sun rasa rayukansu a wannan fadan, wasu guda 27 kuma sun ji rauni
An kwashe wadanda suka ji rauni zuwa jinya, yayin da sojojin ke kokarin bin sawun 'yan ta'addar da suka tsere.
Idan ba a manta ba, 'yan ta'addar Boko Haram sun kai hari har suka kashe wani barden yaki na sojojin Najeriya, Leftana-Kanar mohammed Abu Ali, a garin na Kangarwa.