Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Wasan Chipolopolo Sun Sauka Lusaka Dauke Da Kofin Afirka


Dubban magoya bayan 'yan wasan Zambiya suka yi cincirindo litinin a Lusaka, domin tarbar zakarun na kasashen Afirka
Dubban magoya bayan 'yan wasan Zambiya suka yi cincirindo litinin a Lusaka, domin tarbar zakarun na kasashen Afirka

Dubban jama'a sun yi cincirindo a filin jirgi domin tarbar zakarun wadanda suka ciwo ma kasar Zambiya kofinta na farko na Afirka

Dubban jama'a cikin farin ciki da annashuwa sun yi dafifi domin tarbar 'yan wasan kwallon kafa na Zambiya, wadanda suka ciwo ma kasar kofinta na farko na zakarun nahiyar Afirka.

Litinin 'yan wasan suka sauka a babban filin jirgin saman birnin Lusaka, dauke da wannan kofi na zakarun kasashen Afirka wanda suka yi ta nunawa dubban Zambiyawan da suka taru domin murna.

Kungiyar ta Zambiya, wadda 'yan kasar ke kira "Chipolopolo" ta doke kasar Ivory Coast ko Cote D'Ivoire wadda kwararru suka yi hasashen zata lashe kofin, da ci 8 da 7 a bugun fenariti. An buga wasan na karshe lahadi a Libreville, babban birnin Gabon.

An cika lokaci da kuma karin lokacin da aka yi ba tare da wata kungiya ta jefa kwallo a raga ba. Sai da kasashen biyu suka buga fenariti har sau 18 kafin a samu zakara a tsakaninsu, inda Stophira Sunzu an Zambiya ya buga kwallon da ya ba kasarsa nasara.

Kafin cikar lokacin wasan, Ivory Coast ta samu damar jefa kwallo a raga a lokacin da aka ba dan wasanta Didier Drogba damar bugun fenariti, ya kunma ja gola zuwa gefe guda ya buga kwallon gefe, ga raga fayau, amma sai ya buga kwallon ta yi sama.

Zambiya ta samu nasara a dab da inda wani jirgin sama ya fadi ya kashe 'yan wasan kasar su 25 a shekarar 1993.

'Yan wasan na bana, sun ziyarci bakin teku a kusa da inda jirgin na kasarsu ya fadi shekaru 19 da suka shige.

XS
SM
MD
LG