Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kwastam Ta Yi Babban Kamu a Najeriya


Hamid Ali Mai Ritaya Shugaban Hukumar Kwastam Ta Najeriya
Hamid Ali Mai Ritaya Shugaban Hukumar Kwastam Ta Najeriya

Hukumar kwastam din Najeriya na ci gaba da samun nasara akan masu fasakori, na baya bayan nan shine motoci goma sha biyar da hukumar ta kama a yankin jihohin Oyo da Osun shake da kaya iri iri da kudinsu ya haura Naira miliyan 28.

Shugaban kwastan mai kula da jihohin biyu Udu Aka shi ya gabatarwa taron 'yan jarida ababen da suka kama wadanda inda ya ba da kiyasin kayan.

Aka ya kara da cewa abun damuwa ne wasu 'yan Najeriya marasa kishin kasa sun ki tuba da yin fasakorin kayayyaki duk da gargadin da ake yi masu da asarar da suke tafkawa.

Har ila yau ya kuma ce abun takaici ne wasu mutane musamman dattawa suna zuwa su yi kamun kafa domin a saki haramtattun kayayyakin da aka kama.

Aka ya ci gaba da cewa a tsarin gwamnatin tarayya an hana shigowa da shinkafa ta iyakokin kasa saboda inganta tattalin arzikin kasa.

Haka ma an hana shigowa da tsoffin tayoyi saboda kare lafiyar jama'a tare da inganta ma'aikatun dake sarrafa tayoyi a cikin gida.

Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG