Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Kotu Ta Haramta Yin Amfani Da Sojoji


Babban hafsan tsaron Najeriya, Air Marshal Alex Badeh
Babban hafsan tsaron Najeriya, Air Marshal Alex Badeh

Karar da wani dan majalisar wakilai ya kai na dakatar da gwamatin kan yin amfani da sojoji a lokutan zabe ta yi nasara.

Wata kotu da ke zama a jihar Lagos a tarayyar Najeriya, ta haramta yin amfani da sojojin a zabe mai zuwa yayin da kasar ke tunkarar zabuka a ranar asabar.

Hukuncin ya biyo bayan karar da wani dan majalisar wakilai Femi Baja ya shigar inda ya nemi kotun ta haramtawa sojojin shiga harkokin zabe a kasar.

A cewar mai shari’a Ibrahim Buba, yin amfani da sojoji ranar zabe ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa na shekarar 1999.

Gwamnati dai ta dage sai ta yi amfani da sojojin a lokutan zabe, amma mai shari’a ya yi watsi da wannan bukata, yana mai cewa idan har akwai bukatar hakan har sai ‘yan majalisa sun amince.

Koda yake kotun ta yi la’akkari da cewa shugaban kasa yana da damar ya yi amfani da ikon da doka ta ba shi na tura sojoji domin maido da doka da oda, amma kuma alkali y ace sai dai idan hakan bai karya dokar kasa ba.

Femi Baja dai ya kalubalanci shugaban kasa ne da wasu manyan hafsoshin sojin kasar su biyar a karar da ya shigar na yin amfani da sojoji a lokacin zaben

XS
SM
MD
LG