Tuni uwar jam'iyyar ta kasa ta tura jami'anta jihohi domin su gudanar da bita wa magoya bayanta.
A jihar Gombe, Malam Ibrahim Bulama shi ya gudanar da bitar inda ya ce suna fadakar da mutanen tun daga farkon zabe har zuwa lokacin da za'a kammalashi.
Sun kuma koyawa mutanen yadda za su dangwala yatsunsu da yadda za'a saka katunansu cikin mashin zabe din da kuma yadda naurar zabe za ta tabbatar cewa katinsu ne.
Ya kara da cewa sun yi hakan ne domin tsarin zabe na wannan shekarar ba daya ya ke da na baya ba. Ya ce ba sa son su ragewa kansu kuri'a da kansu.
A shirin sun gayyato mutane biyu daga kowacce mazaba da za su koyar kana su ma su je su fadakar da mutane a mazabarsu.
Sani Dijje shugaban yakin neman zaben gwamna na dan takarar jam'iyyar APC a jihar Gombe ya ce sun shirya wayar da kawunan jama'a ne domin an ga ya da ce su fito su kada kuri'arsu.
Ya ce yadda al'ummarsu ta ke ya kamata a ilmantar da su yana mai cewa shugaban hukmar zabe, Farfesa Attahiru Jega ya fito da tsarin zabe da zai rage magudi ba kamar yadda aka saba ba.
Wasu da suka halarci taron bitar, sun ce sun koyi abubuwa da dama dangane da zaben da za su yi tare da samun fahimta akan yadda na'urar tantance masu kada kuri'a ke aiki.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad.