Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mike Pompeo Da Shugabanin Turkiyya Sun Gana Akan Bacewar Dan Jarida Khashoggi


Mike Pompeo and Melvut Cavusoglu
Mike Pompeo and Melvut Cavusoglu

Hukumomin Saudiyya sun tabbatarwa Mike Pompeo cewa nan gaba kadan zasu bayyanawa duniya hakikanin abinda ya faru da Jamal Khashoggi akan cewa da ransa ya bar karamin ofishin Jakadancin Saudiyya dake Isantanbul.

A yau ne Sakataren Harakokin wajen Amurka Mike Pompeo ya gana da manyan kusoshin gwamantin Turkiyya, ciki har da shugaban kasar, Recep Tayyip Erdogan, jim kadan bayanda ya gama ganawa da shugabannin Saudiyya, wadanda suka tabattar mishi da cewa nan bada dadewa ba zasu nunawa duniya “cikakkiyar shedar” da zata nuna abinda ya faru ga dan jaridar nan na Amurka, Jamal Khashoggi.

Wanda ya bace bayan daya shiga karamin ofishin jakadancin Saudiyya dake birnin Istanbul na Turkiyya. Sai dai kuma Pompeo bai bada wani bayani ba dangane da abinda suka tattauna da Shugaba Erdogan ko ministansa na harakokin waje, Melvut Cavusoglu, kafin ya baro kasar ta Turkiyya.

Shi dai Khashoggi, wanda yayi suna saboda yadda yake yawan caccakar shugabannin Saudiyya, wanda kuma ke yawan rubuta kasidu a jaridar Washington Post, ya bace ne tun ranar 2 ga watan nan na Oktoba, bayanda ya shiga karamin ofishin jakadancin Saudiyya dake Istanbul.

Hukumomin Turkiyya sunce sunyi imani jami’an Saudiyya ne suka kashe Khashoggi a cikin ofishin, amma gwamnatin Saudiyya tace da ransa ya baro ofishin.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG