Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya haramtawa jami’an tsaro da sauran hadimai raka manyan mutane zuwa rumfunan zabe ko wuraren tattara kuri’u yayin zaben gwamnan jihar Ondo.
Kakakin rundunar ‘yan sandan kasar, Olumuyiwa Adejobi, ne ya fitar da sanarwa a yau Alhamis dake cewa, Egbetokun ya dauki “kwararan matakan tsaro” domin tabbatar da an gudanar da sahihin zabe cikin lumana da adalci.
Egbetokun ya kuma tura mukaddashinsa, DIG Sylvester Alabi, a matsayin jami’in da zai kula da zaben tare da sanya idanu wajen aiwatar da dabarun tsaro da tabbatar da doka da oda tsawon lokacin da zaben zai gudana.
Haka kuma babban sufeton ‘yan sandan ya bayyana sunayen AIG Bennett Igweh da CP Tunji Disu, a matsayin mataimakin babban sufeto da kwamishinan ‘yan sandan da zasu taimaka wajen kula da zabe a jihar ta Ondo.
Egbetokun ya kuma ce za’a takaita zirga-zirgar dukkanin ababen hawa a kan tituna da hanyoyin ruwa da sauran nau’ukan sufuri tun daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma a ranar Asabar mai zuwa a fadin jihar in banda masu ayyukan musamman, irinsu motocin daukar marasa lafiya da ‘yan jaridu da kuma jami’an kashe gobara.
Dandalin Mu Tattauna