Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben 2023: Ya Cancanta Goodluck Jonathan Ya Tsaya Takarar Shugaban Kasa?


Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya mika mulki ga Shugaba Muhammadu Buhari
Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya mika mulki ga Shugaba Muhammadu Buhari

Sabuwar muhawara ta kaure tsakanin masanan shari’a da ‘yan siyasa a Najeriya dangane da cancanta ko rashin cancantar sake tsayawa takarar shugaban kasa da ake rade-radin cewa ana zawarcin Goodluck Jonathan ya yi.

Muhawara ta kaure ne dai bayan da aka fara yayata cewa, wadansu masu fada a ji a jam’iyar APC na kokarin jan ra’ayin shugaba Muhammadu Buhari ya yi zawarcin tsohon shugaban kasar, ya canza sheka zuwa APC, ya sake tsayawa takarar shugaban kasa, domin yin shugabancin wa’adin mulki daya, kana ya ba da dama ga wani da zai fito daga Arewa Maso Gabashin kasar ya maye gurbinsa.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun wadansu kungiyoyi tsirarru a sassa daban daban na kasar, da su ka fara fita suna gangamin kira ga tsohon shugaban kasar ya sake neman tsayawa takarar shugaban kasa.

Ranar 27 ga watan jiya wadansu gungun mutane su ka yi gangami tare da ba tsohon shugaban kasar wa'adin kwana 7 ya amsa kiran da ake yi mashi ya nemi tsayawa takara. Kungiyar ta bayyana cewa, ba ta damu da jam'iya ba. cancanta kawai ta ke dubawa.

An kuma yayata bidiyon gangamin da aka ce an gudar a birnin Kano na kira ga tsohon shugaban kasar ya tsaya takara, kamar yadda aka wallafa a @ArewaTwitter.

Jam’iyar PDP ta jima tana ikiririn cewa, APC na zawarcin tsohon shugaban kasar, wanda jigo ne a jam’iyar PDP, yunkurin da masu ruwa da tsaki a jam’iyar PDP su ke bayyana cewa, banda zubar da mutuncin tsohon shugaban kasar, zai kuma toshe wata dama da ke akwai ga wani mai sha’awa daga yankin da ya fito na neman tsayawa takarar shugaban kasa a shekara ta 2027.

An fara rade radin zawarcin tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya koma jam’iyar APC ne tun a shekara ta 2021, lokacin da ake fara yayata cewa, Goodluck Jonathan ya sake sheka zuwa jam’iyar APC a asirce. Sai dai a wata ganawa da manema labarai a Abuja a wancan lokacin, sakatare janar na kwamitin wucin gadi na taron kasa na musamman CECPC, Saneta John James Akpanudoehe ya fitar da sanarwa da ta fayyace cewa, yayinda jam’iyar APC za ta janye wa sabbin shiga wadansu sharuda da ta gindaya, wannan bai nuna cewa Jam’iyar ta tsayar da su takara ba.

Sanarwar ta fayyace cewa, “janye sharudan bai shafi wani mutum guda ba kamar yadda ake shaci-fadi a wadansu wurare. Shiga jam’iyar bai ba wani wata dama ta musamman na zama dan takarar jam’iyar a wani zabe ba. Tilas ne dukan masu sha’awar tsayawa takara su bi tsarin neman tsayawa takara kamar yadda ya ke a kundin tsarin gudanar da harkokin jam’iyar APC.”

Kamar yadda ake fara tallata masu neman tsayawa takara, an fara ganin ana lillika hotunan Goodluck Jonathan ana nuna goyaan bayan ya tsaya neman takara a zaben 2023 a wadansu jihohin arewacin Najeriya.

Tuni ‘yan fafatuka da kuma masu ilimin shari’a da suka hada da fitaccen lauyan kare hakkin bil’adama Femi Falana su ka fara caccakar wannan yunkurin da cewa, tsaida shi takara ko karkashin wacce jam’iya ce ya sabawa tsarin dokar kasa.

Fitaccen Lauya a nahiyar Afurka, Femi Falana, SAN.
Fitaccen Lauya a nahiyar Afurka, Femi Falana, SAN.

A wata rubutacciyar sanarwa da ya fitar, lauya Falana ya bayyana cewa, sashe 137 sakin layi na 3 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya kayyade wa’adin shugabancin Najeriya inda aka bayyana cewa:

“An haramtawa tsohon Shugaban kasa tsayawa takarar neman a zabe shi a wannan matsayin karkashin kundin tsarin mulkin kasa na shekara ta 1999 sashen na 137 (3) wanda ya bayyana cewa.”

“Ba za a zabi mutumin da aka rantsar domin kamala wa’adin mulkin wani da aka zaba a wannan matsayin domin yin fiye da wa’adin mulki daya ba.”

Bisa ga cewar shi, idan Goodluck Jonathan ya sake tsayawa takara aka zabe shi, ya zama ke nan zai yi mulkin Najeriya na tsawon shekaru tara, akasin shekaru takwas da kundin tsarin mulkin Najeriya ya kayyade.

Sai dai wadansu masana shari’a sun bayyana cewa, an yi wa kundin tsarin mulkin kwaskwarima ne bayan shugaba Goodluck Jonathan ya bar mulki sabili da haka, gyaran mai shafe shi ba. Bisa ga cewarsu, ba a komawa da baya a aiwatar da sabuwar doka da aka kafa kan abinda ya faru kafin kafa dokar.

Batun yiwuwar sake tsayawa takarar ta Goodluck Jonathan ta ja hankalin ‘yan Najeriya da dama da suka rika bayyana mabanbantan ra’ayoyi a shafukan sada zumunta. Yayinda wadansu su ke bayyana goyon baya da kira gare shi ya tsaya takara, wadansu suna ganin wannan raguwar dabara ce, kuma ba zai zame mashi alheri ba.

Tsohon dan majalisar dattijai Saneta Shehu Sani ya ce kada Goodluck Jonathan ya yarda a rude shi ya tsaya takara.

Wani wanda ya wallafa hoton Goodluck Jonathan yana tsaye a bayan wadansu da suka yi tattaki zuwa kofar gidansa nuna kira ya fita ya tsaya takara. ya bayyana cewa, da ganin fuskar shi ka san yana cikin tsaka mai wuya.

Gazawar Mulkin Jonathan

Masu kula da lamura sun bayyana Goodluck Jonathan a matsayin Karen da baya iya haushi balle cizo. Suna zargin cewa, ya nuna halin ko in kula da kuma rashin karfin halin tsautawa da sa ido kan yadda mukarrabansa da manyan jami’an gwamnati da suka hada da ministoci, da masu bashi shawarwari na musamman, da kuma mataimakansa na musamman suka gudanar da ayyukansu.

Bisa ga cewarsu, ya nuna sakaci ta wajen sakar masu kota suka rika cin karensu ba babbaka, lamarin da ake gani ya ruruta cin hanci da rashawa da wawurar kudin gwamnati, da kuma assasa matsalar tsaro.

Idan za a iya tunawa jim kadan bayan rantsar da gwamnatin Buhari da ta gaji Jonathan aka fara bin diddigin wadansu fitattun jami’an gwamnatin Jonathan da ake zargi da rub da ciki da biliyoyin Naira, da suka hada da tsohon mai ba gwamnati shawarwari kan harkokin tsaro Sambo Dasuki da aka zarga da batar da sama da dalar Amurka biliyan biyu na sayen makamai da ake ba lakabi da “Dasukegate https://en.wikipedia.org/wiki/$2_billion_arms_deal), da kuma tsohuwar Ministar Mai Diezani Alison-Madueke da aka zarga da wawurar kimanin dalar Amurka biliyan 20.

TSohuwar Ministar albarkatun mai Diezani Alison-Madueke
TSohuwar Ministar albarkatun mai Diezani Alison-Madueke

An kuma zargi shugaba Jonathan da rashin kyakkyawan sa ido kan harkokin tsaro duk da makudan kudaden da gwamnati ta kashe a fannin, lamarin da ya ruruta ayyukan kungiyar Boko Haram, da ya kai ga sace daliban makaranta ‘yan mata 276 a wata makarantar kwanan dalibai da ke garin Chibok, da masu kula da lamura ke cewa, rashin daukar matakin gaggawa ya sa aka gaza ceto su.

Ana kuma zargin tsohon shugaban kasar da zama dan amshin shatan ‘yan siyasa musamman na arewacin Najeriya da suke jan igiyar mulki daga nesa suna sa shugaban kasar ya yi yadda su ke so.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi amfani da wadannan hujjojin a yakinshi na neman zabe, inda ya yi alkawarin shawo kan matsalar tsaro da kuma gudanar da mulkin ba sani ba sabo a fannin yaki da cin hanci da rashawa, manyan matsaloli da su ka tsonewa ‘yan Najeriya ido tun zamanin mulkin Goodluck Jonathan har I zuwa yanzu.

A hirar shi da Muryar Amurka, wani mai zaman kansa kuma shugaban kungiyar lauyoyi a jihar Plato Yakubu Saleh Bawa ya bayyana cewa, idan har da gaske jam’iyar APC tana zawarcin tsohon shugaban kasar ya tsaya takara karkashin tutar jam’iyar, ya nuna ke nan, jam’iyar ta amince da gazawar gwamnatin Buhari ta kuma goyi bayan masu cewa, jiya tafi yau.

Buhari, hagu, Jonathan dama (Facebook/Bashir Ahmad)
Buhari, hagu, Jonathan dama (Facebook/Bashir Ahmad)

Nasarorin Mulkin Jonathan

Duk da kurakuran da masu kula da lamura su ka ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya tafka a zamanin mulkinsa, an kuma yaba nasarori da ya samu a bangarori da dama da ya hada da amsa shan kayen zabe tun kafin hukumar zabe ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasa a shekara ta 2015, abinda ya zama tarihi a siyasar Najeriya musamman ga wanda yake rike da mulki.

Masu sharhi kan lamura na kuma bayyana cewa, gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ta sami gagarumar nasara idan aka kwatanta da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari. Daga cikin muhimman batutuwa da suka Ambato da suka ce jiya ta fi yau kyau, akwai batun matsalar tsaro da a lokutan baya ake kushewa gwamnatin Jonathan da gazawa. An kuma bayyana ci gaban mai shiga rijiya a fannin yaki da cin hanci da rashawa da kuma harkokin siyasa, damokaradiya da kuma zabe, idan aka kwatanta abinda ya wakana a zamanin mulkin Jonathan da abinda ke faruwa a karkashin mulkin shugaba Buhari.

Oronto Douglas
Oronto Douglas

A shekara ta 2012, gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ta fitar da wani bayani mai tsawon shafi 157 da mai ba shugaban kasar shawarwari na musamman kan bincike da tattara bayanai Oronto Douglas ya ce “ a cikin shekaru biyu da fara wa’adin mulkinsa, shugaba Goodluck Jonathan ya kafa fandeshan mai karfi na bunkasa fannonin nona, kiwon lafiya, harkokin albarkatun man fetir, sufurin jiragen sama, ilimi, wutar lantarki, da kuma wadansu muhimman bangarorin da su ka shafi tattalin arzikin kasa,” bangarorin da masu kula da lamura su ke jinjinawa tsohuwar gwamnatin yanzu, idan aka kwatanta da gwamnatin Buhari.

Downloads/President_Jonathan's_Progress_Report.pdf

Tuni wadansu shugabannin addinai suka fara “anabcin” cewa, Goodluck Jonathan zai zama shugaban kasa idan ya sake tsayawa takara. Wani abu da ya zama ruwan dare a Najeriya inda a lokutan zabe wadansu shugabannin al’umma da na addinai su ke fita suna bayyana cewa, suna da haikinin cewa, wani dan takarar zai lashe zabe amma a sami akasin haka.

I zuwa yanzu, tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan bai fita fili ya karyata ko kuma tabbatar da wadannan rade radin ba, banda kawai ambaton sa da cewa, “a jira a gani.”

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG