'Yan siyasan sun bayyana mabanbantan ra'ayoyin a wani zaman tattaunawa da Muryar Amurka da Shirya a birnin tarayya Abuja da taken, "hasashen ma’abota jam’iyyu kan irin tasirin da su ke ganin suna da shi a zaben 2023."
A lokuta da dama a baya, irin wannan zauren kan hargitse, saboda wani ya ambaci wani ra’ayi da ya saba da muradan sauran jam’iyyun, amma a wannan karon akalla kowa ya samu damar nuna cewa gwaninsa ne zai iya lashe zaben da za a gudanar a ranar 25 ga watan nan na Fabrairu.
Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, daga jihar Neja, ya ce yana da kyau a mara baya ga dan takarar APC Bola Ahmed Tinubu don hakan ya zama nuna karamci musamman daga yankin arewa a kan yadda Tinubu ya mara baya ga shugaba Buhari ya samu karin tagomashin da ya ba shi damar lashe zabe a 2015.
Nan take shi kuma Sabo Imamu Gashua, wanda a baya dan gani-kashenin shugaba Buhari ne, ya ce APC da PDP sun gaza kuma lokaci ya yi da za a gwada Rabi’u Musa Kwankwaso na NNPP, don ba ya saba alkawari kuma yana damuwa da bukatun al’ummarsa.
Dan kwamitin zaben fidda gwani na APC wanda Tinubu ya lashe, Muhammad Saleh Hassan, ya ce a gaskiya ba shi da shaidar zargin da a ke yi cewa an yi amfani da kudi wajen sayen wakilan zabe amma duk da haka yace kowa ya zabi wanda yake so.
A nasa bayanin jami’in tara kudi a ofishin goyon bayan shugaba Buhari, Ibrahim Hussaini Abdulkarim, ya ce shi tuni ya dawo daga rakiyar APC da salon mulkin shugaba Buhari, don haka yanzu shi daraktan kamfen dan takarar jam’iyyar Labour Peter Obi ne.
Abdulkarim ya ce zargin da a ke yi wa wasu magoya bayan Obi cewa suna da muradin kafa kasar Biafra ba gaskiya ba ne, kuma ko da gaskiya ne adadin yawan mutanen da aka kashe a arewa daga miyagu ‘yan arewa ya linka kisan da miyagun Biafra suka yi.
Duk wadanda suka halarci zauren sun samu damar bayyana ra’ayinsu kan dalilan da suke ganin gwanayensu ne suka fi cancantar karbar ragamar mulki bayan kammala wa’adin shugaba Buhari.
Saurari rahoton Hauwa Umar: