Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben 2023: INEC Ta Hada Gwiwa Da MTN, Glo, Airtel Da 9Mobile Don Kaucewa Matsalar Internet A Ranar Zabe


Shugaban hukumar zabe ta INEC a Najeriya, Farfesa Mahmood Yakubu
Shugaban hukumar zabe ta INEC a Najeriya, Farfesa Mahmood Yakubu

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta INEC ta ce tana aiki kafada da kafada da kanfanonin sadarwa kamar su MTN, Glo, Airtel da 9Mobile domin magance duk wata matsalar hanyar sadarwar internet da ka iya tasowa yayin kada kuri’a.

Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a jiya Juma’a a wani taron manema labarai a birnin Abuja.

Farfesa Yakubu ya tabbatar da cewa hukumar ta kuma dauki isassun matakan karfafawa da kare na’urori da ayyukanta daga munanan hare-haren masu kutse.

Ya kara da cewa INEC tana da kwarewa sosai wurin tura sakamakon zabe ta manhajar iREV, yayin da na’urar tantance masu kada kuri’a ta BVAS abin da kawai take bukata shine layin sadarwar yanar gizo daga runfar zabe.

“Mun dauki kwararan matakai na karfafawa da kuma kare na’urori da ayyukan mu. Ina kara tabbatar da cewa mun kammala duk shirye-shiryen mu a bangaren tsaron yanay gizo, saboda akwai masu liken asiri amma al’ummar Najeriya su kwantar da hankalin su, saboda layukan mu suna karfin da zasu jure hare-hare amma dai mun dauki kwararan matakai”, in ji Farfesa Yakubu.

A cewarsa, “dama na’urar BVAS ba ta lantarki bane, ba zata aiki da layin internet ba a ranar zabe. Mashinan ba za su yi aiki da layin sadarwa kwata-kwata ba. Inda za a bukaci hada na’urar da layin internet kadai shine lokacin da za a tura sakamakon daga matakin runfar zabe kuma mun gama wannan tanadin”, yana kara tabbatarwa da ‘yan Najeriya.

XS
SM
MD
LG