Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Paparoma Francis Ya Yi Hudubar Farko a Amurka


Paparoma Francis a sujada
Paparoma Francis a sujada

Paparoma Francis ya yi hudubarsa ta farko a nan Amurka a cikin yanayi mai daraja da annashuwa.

Inda aka dinga kada kararrawar coci caco hade da baitukan bauta mai daraja ta farko anan Amurka.

Dubban jama’a sun halarci taron da aka yi a babbar Cocin kasa ta Basilica. Fafaroman ya tabo maganar yada busharar farko a inda ake kira Califonia a yanzu.

Wanda Masu Busharar Sifaniyawa suka fara, mai cike da sarkakiya a karni na 18 karkashin jagorancin Junipero Serra.

Cikin halin dattaku, Fafaroman yayi watsi da zargin da ake wa Serra na musgunawa, inda yace, ya ma kare martabar mutanen kasar ne, sannan shi misali ne na gari don samun ci gaba.

Limamin Kiristan ya yi nasiha game da kwadayin abin duniya, tare da kawo batun yanayi da kuma tausayin masu yiwuwar fadawa cikin wata barazanar rayuwa.

Ya karkare da kira ga mabiyan da su zama masu neman rayuwa mai ma’ana ba ta tinkaho ba, domin samun kwanciyar hankali.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG