Inda a wannan karo yace lallai akwai alamun za’a kara wa’adi na maganar dokar tabaci a yankin arewa maso gabashin Najeriya,inda ‘yan boko haram suka addabi mutane.
Yana mai jaddada cewar lallai kara wannan dokar ba zai sa a canja gwamnonin ba da aka saba a turbar damakradiya a wannan yankin ba.
Ya kuma kara da cewa dajin nan na sambisa duk da kuwa tsananinsa da mahimmashin sa ga ‘yan kungiyar boko haram baza a kai masa hare-hare ba domin kada a cutar da wadansu wadanda basu san hawaba ko saukaba sai dai a ci gaba da samun bayanai da hikimomi na yakan wannan matsala batare da an abka masaba.
Dangane da jawaban da shugaban kasa yayi masu dama ne,na tuntubi daya daga cikin matasa masu fashi baki a Najeriya, Malam Hudu Khalid,domin jin abunda ya fahimta.
Yace ”na dauki jawabi a matsayin fuskoki biyu na farko a kwai wasu kalamai da shugaban kasa yayi wanda zan iya cewa yayi su a dai dai,amma akwai kurakure a cikin jawabi sa a gaskiya.”
Na farko “zan fara bayani akan ma’aikata a kwai rufe Abuja da yace za’a yi na tsawon kwanaki uku, yayi Magana cewa akwai ma’aikata wadanda ya zamo wajibi suje aiki Kaman jami’an tsaro da jami’an gwamnati manya-manya yayi dai-dai,"
"Inda naga cewa bayanin shi basu yi dai-dai ba shine game da dakatar da wadanda zasu shigo cikin garin Abuja masamman masu zuwa neman abinci," inji Hudu Khalid.